Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya amince da murabus din Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, tare da amincewa da nadin Tunji Disu a matsayin mukaddashin Sufeto Janar na ’Yan Sanda nan take.
A baya dai Egbetokun ya mika takardar murabus dinsa ranar Talata, yana mai bayyana wasu muhimman dalilai na iyali.
Cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, ya ce Shugaban kasar ya karbi takardar murabus din tun da safiyar Talata, tare da nuna godiya kan hidimarsa ga kasa.
Sanarwar ta ce Shugaban kasar ya yaba wa Egbetokun kan shekaru masu yawa na hidima mai nagarta ga Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da kasa baki daya, tare da jinjina masa kan kwarewa, jajircewa da kuma kokarinsa wajen karfafa tsarin tsaron cikin gida a lokacin da yake kan mukami.
Sanarwar ta kara da cewa, la’akari da kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a halin yanzu, da kuma bisa tanadin dokoki da shawarwarin doka, Shugaban kasar ya amince da nadin Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Tunji Disu, a matsayin mukaddashin Sufeto Janar nan take.
A cewar sanarwar Shugaban kasar na da yakinin cewa gogewa da kwarewar Disu, da kuma irin jagorancin da ya nuna, za su ba Rundunar ’Yan Sandan Najeriya kwakkwaran shugabanci a wannan lokaci mai muhimmanci.
Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa bisa tanadin Dokar ’Yan Sanda ta 2020, Shugaban kasar zai kira taron Majalisar ’Yan Sandan Najeriya nan ba da jimawa ba domin duba nadin Disu a matsayin cikakken Sufeto Janar, kafin a mika sunansa ga Majalisar Dattawa domin tantancewa.
Shugaban kasar ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta tsaron kasa, karfafa hukumomi, da tabbatar da cewa Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta kasance mai kwarewa, rikon amana, kuma a shirye take wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata.













































