Rundunar ‘Yan sandan Jihar Zamfara ta kubutar da mutune 39 wadanda aka yi garkuwa da su*

Rescued abducted Zamfara victims 678x381 1
Rescued abducted Zamfara victims 678x381 1

Rundunar ‘yan sanda sun ceto mutane 39 da aka yi garkuwa da su a jihar Zamfara ranar Lahadi, tare da kama mutane 10 da ake zargi da hannu a cikin haramtacciyar kungiyar ‘Yankasai’.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Eyuba Elkanah, ne ya bayyana haka ranar Litinin a Gusau.

Ya ce jami’an tsaro sun ceto wadanda aka sace a watan daya gabata na Maris da kuma farkon watan da muke ciki na Afrilu a kauyuka da wurare daban-daban cikin kananan hukumomin Bungudu da Maru na jihar.

“Wadanda aka ceto maza takwas ne, mata 15 ciki har da mata masu shayarwa, da kuma yara 16.

“Rundunar ‘yan sanda hadin gwiwa da tawagogin likitocin gwamnatin jihar sun bawa wadanda aka sace din, taimakon gaggawa.

“Za a mika su ga jami’an kananan hukumomin biyu domin hada su da iyalansu,” inji shi.

Ayuba Elkanah ya kara da cewa, ‘yan sandan sun kuma kwato bindigogi kirar gida da mota kirar Honda 2012 da aka sace da kuma babura hudu da sauran kayayyaki.

Kwamishinan ya kara da cewa, “Akwai ci gaba da aikin share fage na rundunar ‘yan sanda da sojoji a sansanin Dabar Magaji da ke dajin Kadanya tsakanin kananan hukumomin Kaura Namoda da Maradun,” inji kwamishinan ‘yan sandan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here