Gwamnatin Jihar Legas ta nuna alhini kan mutuwar wani jami’in Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Legas da wasu mutum biyu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a mahadar Badagry zuwa Seme ranar Litinin, 23 ga Fabrairu, 2026.
A cikin wata sanarwa daga LAST MA, hukumar ta tabbatar da cewa hatsarin ya shafi wata babbar mota kirar SHACMAN dauke da kaya ta kamfanin Dangote.
Rahoton farko ya nuna cewa motar ta samu matsalar birki yayin da take gudu, lamarin da ya sa direban ya kasa sarrafa ta.
Motar ta bugi jami’in da ke bakin aiki yana kula da zirga-zirga, tare da wani mai tafiya a kafa a mahadar, kafin ta ci gaba da tafiya ta sake buge wani mutum kimanin mita 200 daga wurin.
Dukkanin mutanen uku sun mutu sakamakon munanan raunuka.
Direban ya tsere daga wurin amma daga baya jami’an LASTMA suka kama shi tare da mika shi ga ’yan sanda.
Jami’an ceto da suka hada da na LASTMA, ’yan sanda, Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa da Hukumar Tsaro da Kare Lafiyar Jama’a sun isa wurin, inda aka kai gawarwakin asibiti kuma aka tabbatar da mutuwarsu.
Babban Manajan LASTMA, Olalekan Bakare-Oki, ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi, yana mai cewa jami’in ya rasu ne yayin da yake bakin aiki.
Ya ce hatsarin ya sake nuna hadarin da jami’an zirga-zirga ke fuskanta a kullum, tare da kira ga masu safarar kaya da su bi ka’idojin tsaro yadda ya kamata.
Ya kara da cewa matsalolin na’ura, musamman lalacewar birki, na daga cikin manyan abubuwan da ke jawo munanan hadura a titunan Legas.
An kwace motar da ta haddasa hatsarin tare da mika ta ga rundunar ’yan sanda ta Badagry domin gudanar da bincike.
Hukumar ta ce za ta hada kai da sauran hukumomi domin tabbatar da daukar mataki tare da hana sake faruwar irin wannan lamarin.













































