Gwamnatin Jihar Kano ta kafa wani babban kwamiti mai mambobi 23 domin sa ido kan rabon Naira Biliyan 8 da kayayyakin tallafi ga wadanda gobarar Kasuwar Singer ta shafa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya ruwaito cewa gobarar, wadda ta tashi a sassa daban-daban na kasuwar a lokuta biyu, ta jawo asarar dukiyoyi da jarin kasuwanci na Biliyoyin Naira.
Yayin kaddamar da kwamitin a ranar Talata a Kano, Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Faruq, ya ce an dora wa kwamitin alhakin tabbatar da an raba tallafin cikin adalci da gaskiya.
Umar Faruq, wanda Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Maude, ya wakilta, ya ce an zabo mambobin kwamitin daga fannoni daban-daban masu muhimmanci domin tabbatar da sahihanci da rikon amana wajen gudanar da aikin.
A cewarsa, kwamitin wanda Sakataren Gwamnatin Jihar ke jagoranta, zai tabbatar da gaskiya, adalci da rikon amana wajen rabon tallafin ga wadanda abin ya shafa na hakika.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da kwamishinoni, wakilan Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar, rundunar ’yan sanda, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, Majalisar Masarautar Kano, shugabannin addini da wakilan ’yan kasuwar da gobarar ta shafa.
Ya ce kwamitin zai tantance girman barnar da aka yi, ya auna asarar kayayyaki da jarin da ’yan kasuwa suka yi, tare da tsara hanyar da za a bi wajen rabon tallafin yadda ya kamata.
Sakataren ya kara da cewa kwamitin zai duba matsalolin da ke cikin kasuwar tare da bayar da shawarwari kan hanyoyin hana sake aukuwar gobara a nan gaba.
Ya ce daga cikin aikace-aikacen kwamitin akwai tabbatar da raba tallafin cikin lokaci, da kuma tuntubar masu ruwa da tsaki da kafafen yada labarai domin kara gina amincewar jama’a.
Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwar Kano, Alhaji Sabi’u Bako, ya yaba wa gwamnan jihar kan daukar mataki cikin gaggawa da kuma kafa tsari mai kyau na rabon tallafin.
Ya kuma gode wa Gwamnatin Tarayya bisa aiko da tawaga domin jajanta wa wadanda abin ya shafa, yana mai cewa kwamitin zai gudanar da aikinsa cikin adalci da gaskiya.
Ya ce ko da yake ba a kai ga tantance adadin ’yan kasuwar da gobarar ta shafa da kuma jimillar asarar da aka yi ba, kwamitin zai tabbatar da cewa wadanda aka tantance ne kawai za su amfana da tallafin.
Rahoton ya kuma nuna cewa Shugaban Kasa, Bola Tinubu, ya amince da bayar da Naira Biliyan 5 a matsayin tallafin rage radadi ga ’yan kasuwar da abin ya shafa.
Haka kuma, Kungiyar Gwamnonin Jam’iyya Mai Mulki ta APC ta bayar da Naira Biliyan 3 domin tallafa wa wadanda abin ya shafa da kuma taimakawa farfadowar kasuwancin su.
Tun da farko, wadanda gobarar ta shafa sun karbi Naira Miliyan 200 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, domin rage musu radadin asarar da suka yi.













































