Kotu ta dage lokacin sake gurfanar da El-Rufai

El Rufai in ICPC custody 750x430

An dage sauraron gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a ranar Laraba a Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, bayan da bangaren kariya ya kasa gabatar da shi a gaban kotu.

Ana tuhumar El-Rufai da laifuffuka uku da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta shigar a kansa, bisa zargin satar sauraron wayar Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu.

A zaman kotun na ranar Laraba, lauyan kare shi, Oluwole Iyamu, ya shaida wa kotu cewa abokin aikinsa yana tsare a hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaka da Haka, don haka ba a samu damar kawo shi kotu domin a gurfanar da shi ba.

Ya roki kotun da ta dage shari’ar domin ba da damar gabatar da shi, sannan ya nemi a saurari bukatar beli, yana mai cewa bangaren masu kara ya nuna ba zai yi adawa da bayar da belin ba tunda laifukan na da damar beli.

Sai dai lauyan masu kara, Oluwole Aladedoye, ya bukaci kotun ta dakatar da sauraron batun beli, yana mai cewa ba a riga an gurfanar da wanda ake kara ba.

A takaitaccen hukunci da ta yanke, Mai Shari’a Joyce Abdumalik ta ce tunda ba a yi masa gurfanar hukuma ba tukuna, to bukatar beli ta yi wuri.

Daga nan kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 23 ga Afrilu, 2026, domin gurfanar da shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here