Kotun Kano ta tura wata ‘yar kasar Sin gidan gyaran hali kan zargin zamba da lalata kadarori

Kano High Court (1)

Babbar Kotun Jihar Kano a ranar Talata ta bayar da umarnin tsare Zhang Qunfang, wata ‘yar kasar Sin, a gidan gyaran hali kan zargin zamb cikin aminci da kuma lalata kadarorin kamfanin Huafei International Nigeria Ltd., dake lamba 52 kan titin Hadejia, yankin Gezawa, Kano.

A lokacin gabatar da ita a gaban Mai Shari’a Ma’aji, lauyan masu gabatar da kara Eristio Asaph daga sashen shari’a na hedkwatar ‘yan sanda ya gabatar da takardar tuhuma da aka shigar ranar 3 ga Oktoba, 2024, tare da neman izinin kotu don a karanta wa wadda ake zargi tuhumar.

Sai dai lauyan wanda ake kara, Ibrahim Abdullahi Chedi, ya yi watsi da bukatar a karanta tuhume-tuhumen, yana mai cewa ba a kai lokacin gurfanar da ita ba saboda an isar mata da takardun tuhumar ne a ranar da aka zo kotun.

Ya bayyana cewa an kama Qunfang ne a Abuja ta hannun INTERPOL, sannan aka ba ta beli na lokaci-lokaci, kuma bisa doka ta ACJL 2019, sashi na 127 sakin layi na 2, ya kamata a isar mata da takardar tuhuma a kalla kwanaki bakwai kafin a gurfanar da ita.

Sai dai lauyan masu gabatar da kara ya mayar da martani yana mai cewa Qunfang ta ki karbar takardun tuhume-tuhumen bayan an sake ta bisa beli.

Bayan la’akari da duka bangarorin biyu, Mai Shari’a Ma’aji ya bayar da izinin a karanta tuhume-tuhumen guda biyu da ake yi wa wadda ake zargi.

Takardar tuhumar ta nuna cewa Qunfang ta yi amfani da sunan wani abokin kamfani, Mista Zhu Bin, ta hanyar yin cuwa-cuwa domin ta saka sunanta a matsayin mai sa hannu kan kudaden kamfanin, sannan ta cire dalar Amurka $80,000 daga asusun kamfanin ba tare da amincewar sauran daraktocin kamfanin ba. Bugu da kari, tana da laifin rushe wani gini na Huafei International Nigeria Ltd.

Masu gabatar da kara sun bayyana cewa wadannan laifuka sun saba da sassa na dokar Penal Code. Qunfang ta musanta laifin.

Kotun ta daga zaman zuwa ranar 1 ga Nuwamba, 2024, don sauraron bukatar belin, tare da bayar da umarnin ci gaba da tsare ta a gidan gyaran hali kafin wannan lokaci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here