Zargin badaƙala: Dangote ya shigar da ƙorafi a kan tsohon shugaban NMDPRA Farouk Ahmed a gaban EFCC

Dangote Farouk

Shugaban rukunin kamfanin Dangote Aliko Dangote, ta hannun lauyansa, ya shigar da ƙorafin cin hanci da rashawa kan tsohon daraktan gudanarwa na Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa NMDPRA, Farouk Ahmed, a hedkwatar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Manyan Laifukan Kudi EFCC.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa wannan mataki ya biyo bayan janye irin wannan ƙorafi da Dangote ya gabatar a gaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaƙa ICPC, a matsayin dabara ta gaggauta gurfanar da wanda ake zargi a gaban shari’a.

A cikin ƙorafin da babban lauyan Dangote Dakta O.J. Onoja SAN ya sanya wa hannu, Dangote ya bukaci EFCC ta binciki zargin cin zarafin mukami da tara dukiya ta haramtacciyar hanya da ake yi wa Farouk Ahmed, tare da gurfanar da shi idan bincike ya tabbatar da laifinsa.

Ƙorafin ya kuma bayyana cewa Dangote zai gabatar da hujjoji da za su tabbatar da zargin almundahana da nuna halin raina doka.

Ƙorafin ya jaddada cewa EFCC tare da sauran hukumomin haɗin gwiwa na da cikakken matsayi wajen gurfanar da masu aikata laifukan kuɗi da cin hanci da rashawa, kuma idan aka kafa hujjar farko ta laifi, kotuna ba sa jinkirin hukunta masu laifi, kamar yadda shari’o’in Lawan da gwamnatin tarayya da Shema da gwamnatin tarayya suka nuna.

Karanta: Zargin almundahana: Hukumar ICPC ta ci gaba da bincike duk da janye ƙorafin Dangote

Haka kuma, lauyan ya bukaci EFCC karkashin jagorancin Olanipekun Olukoyede da ta binciki ƙorafin cin zarafin mukami da rashawa da ake yi wa Injiniya Farouk Ahmed tare da gurfanar da shi idan aka same shi da laifi.

Ƙorafin ya ƙara da cewa gaggauta daukar mataki kan wannan batu ba wai kawai wajibi ba ne, har ma zai zama darasi ga sauran jami’an gwamnati masu irin wannan dabi’ar cin hanci.

Ci gaban wannan lamari ya kara nuna kudurin Dangote na gaskiya da rikon amana a bangaren man fetur da iskar gas na Najeriya.

A ranar 14 ga Disamba 2025, Dangote ya bayyana damuwa kan mu’amalar kuɗin Farouk Ahmed, inda ya yi zargin cewa tsohon jami’in yana rayuwa fiye da karfin kudaden halal dinsa.

Dangote ya bayyana cewa ‘ya’yan Farouk Ahmed hudu sun yi karatun sakandare a manyan makarantu masu tsada a kasar Switzerland, lamarin da ya ci kudade masu yawa na miliytoyin daloli.

Ya lissafa sunayen makarantu da ‘ya’yan suka halarta, tare da bayanin cewa kowanne yaro ya shafe shekaru shida a wadannan makarantu, inda aka kiyasta kudin karatu, tafiye-tafiye da kula da kowanne yaro a Dalar Amurka Dubu Ɗari Biyu a shekara, wanda ya kai kusan Dalar Amurka Miliyan Biyar gaba daya.

Dangote ya kuma yi zargin cewa an kashe karin Dalar Amurka Miliyan Biyu wajen karatun jami’a na ‘ya’yan, ciki har da Dalar Amurka Dubu Ɗari Biyu da Goma da aka kashe kan shirin MBA na Faisal Farouk a Jami’ar Harvard a shekarar 2025.

Ya nuna cewa ya dace ‘yan Najeriya su san tushen wadannan kudade, musamman ganin yadda iyaye da dama a Jihar Sokoto ke fama da wahalar biyan kudin makaranta kadan.

Ƙorafin ya bukaci cikakken bincike domin tabbatar da adalci da dawo da amincewar jama’a ga hukumomin kula da harkokin kasa na Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here