Rahoton da ya bazu a shafukan sada zumunta yana iƙirarin cewa tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, na shirin auren tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, an tabbatar da cewa ƙirƙira ce gaba ɗaya bayan binciken da PRNigeria ta gudanar.
Jita-jitar, wadda ta samu karɓuwa sosai a dandali irin su Facebook da X, ta zo ne tare da wani hoto da aka gabatar a matsayin hoton shirin aure na mutanen biyu.
Tuni dai aka yi ta yaɗa sakon ta wasu shafuka ciki har da Adamawa Pulse, inda ya samu dubban martani da rabawa, musamman duba da cewa Aisha Buhari ta kammala iddarta ta Musulunci bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a watan Yuli na shekarar 2025.
Haka kuma, an ƙara yaɗa hoton ta hannun wasu fitattun mutane a idon jama’a, ciki har da Sanata Shehu Sani da ɗan siyasar Arewa Magaji Muazu, lamarin da ya ƙara tayar da hasashe da ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma.
Wannan jita-jita ta bayyana ne watanni bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a birnin London yana da shekaru 82 a duniya.
Muhammadu Buhari, wanda ya auri Aisha Buhari a shekarar 1989, ya bar matarsa da ’ya’ya takwas da jikoki da dama.
Aisha Buhari ta kammala iddarta ta Musulunci a ranar 18 ga Nuwamba, 2025, lamarin da ya sa aka fara yaɗa hasashen yiwuwar sake aurenta a internet.
Sai dai cikakken bincike da PRNigeria ta gudanar, tare da amfani da binciken fasahar tantance hotuna na zamani, ya tabbatar da cewa hoton da ake yaɗawa ƙirƙira ne, kuma iƙirarin da aka jingina masa ba shi da tushe.
Binciken ya nuna shafukan sada zumunta na na Aisha Buhari da Isa Ali Pantami bai nuna wata sanarwa, alama ko nuni da ke goyon bayan shirin aure ba, haka kuma binciken kalmomi a kafafen labarai masu inganci bai samar da wata shaida da ke tabbatar da iƙirarin ba.
Binciken fasahar tantance hotuna na InVid da na gano hotunan da aka ƙirƙira da basirar kere-kere ya nuna cewa hoton da ake kira hoton shirin aure an yi masa gyaran da fasahar zamani ne, inda aka ɗora fuskokin tsohon ministan da tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa a cikin wani tsari na biki.
Haka kuma, wani sabon littafin tarihin rayuwar Muhammadu Buhari mai shafi 600, wanda Dakta Charles Omole ya wallafa, ya bayyana cewa Aisha Buhari ba ta da shirin sake aure, inda ta zaɓi mayar da hankali kan iyalinta da ayyukan gidauniyarta.
Sakamakon rashin kowace sahihiyar shaida da kuma ƙaryatawar da ta fito daga manyan tushe masu ƙarfi, PRNigeria ta kammala da cewa iƙirarin da ya bazu a internet ƙarya ne kuma mai ruɗani, tare da tabbatar da cewa hoton da ake yaɗawa an ƙirƙire shi ne ta hanyar fasahar kere-kere.













































