Uwargidan shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, a ranar Alhamis a jihar Gombe ta ƙaddamar da shirin raba “Audugar Mata” kyauta domin ’yan makaranta mata, da nufin inganta tsabtar al’ada, mutunci da kuma iliminsu.
An gudanar da shirin ne ƙarƙashin shirin “Tafiya da ƙwarin Gwiwa” da ke ƙarƙashin “Shirin sabon fatan na Uwargidan shugaban ƙasa.
Ta bayyana cewa shirin zai bai wa ’yan makaranta mata kimanin 370,000 a faɗin ƙasar nan kayan tsabtar al’ada na shekara guda.
A cewarta, kowace jiha 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT) za su karɓi 10,000 ta ofishin uwargidan gwamnan jiharsu.
Ta gode wa Gwamna Inuwa Yahaya da uwargidansa bisa tarbar da suka yi mata da kuma jajircewar da suka nuna wajen tallafa wa ’yan mata.
Ta bayyana shirin a matsayin babban sauyi da zai dawo da kwarin gwiwar ’yan mata da kuma kare iliminsu.
A cewarta, fiye da Naira biliyan 2.5 aka ware domin samar da kayan tsabtar da rarraba su a ƙasa baki ɗaya.
Ta yi gargaɗi kan kau da kai daga shirin ko sayar da kayan da aka raba.
Karanta: Hukumar jin daɗin Alhazai a Kano ta sanya wa’adin rufe biyan kashi 50 cikin 100 na kujerun Hajjin 2026
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya yaba wa uwargidan shugaban ƙasa bisa hangen nesanta, yana mai cewa an haɗa darussan tsabtar al’ada cikin kundin karatu na firamare da sakandare, musamman a fannoni na kimiyyar lafiya.
Ya ƙara da cewa gwamnati na aiki da hukumomi domin inganta ababen more rayuwa na tsafta a makarantu.
Uwargidan gwamnan Gombe, Hajiya Asma’u Yahaya, ta gode wa Reni Tinubu bisa himmarta wajen magance matsalolin da ke shafar mata da ’yan mata.
Ta ce rashin samun kayan tsabtar al’ada da wuraren tsafta na iya jawo yarinya ta rasa akalla kwanaki biyar a kowane wata na karatunta.
Ta yi kira da a kawar da al’adu masu cutarwa da ke hana ’yan mata ci gaba, tare da tabbatar da cewa kowace yarinya tana samun kayan mutunci da damar zuwa makaranta ba tare da tsoro ba.
NAN