Hukumar NAFDAC ta rufe manyan kantunan kasar China guda biyu a Abuja

NAFDAC SEALS 750x430

Hukumar kula da kayayyakin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) a ranar Alhamis ta rufe manyan kantunan kasar China guda biyu da ke Jabi, Abuja, bisa zargin sayar da kaya marasa lasisi a Najeriya.

Kantunan da aka rufe suna kan titin Mike Akhigbe mai lamba 40 da kuma titin Ebitu Ukiwe mai lamba 61, duk a Jabi, inda hukumar ta gano ana sayar da kayayyaki da ba su samu amincewar gwamnati ba.

Haka kuma, hukumar ta rufe wasu shaguna guda takwas a kasuwar Wuse da ake zargin suna sayar da kwayoyi masu karfafa sha’awa.

Rahoton ya nuna cewa shagunan suna kuma sayar da sinadarai masu hadari da ake amfani da su wajen kara girman jiki, ciki har da nono da kuma duwawu, wadanda aka ce suna dauke da guba.

Shugaban sashen bincike da aiwatarwa na hukumar a Abuja, Mista Embugushiki-Musa Godiya, ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan korafe-korafen jama’a.

Karin karatu: Uwargidan shugaban ƙasa ta ƙaddamar da shirin raba “Audugar Mata” kyauta ga ’yan makaranta mata

Ya ce kayayyakin da aka kwace a lokacin samamen sun kai kimanin naira miliyan 170, inda ya bayyana cewa masu sayar da su suna ikirarin likitoci ne su, da kuma masu bada magani ga ‘yan kasa ba tare da cancantar yin hakan ba.

Godiya ya kara da cewa hukumar ta samu bayanai daga jama’a kan cewa wasu ‘yan kasar waje da ke da kantuna a Abuja sun shigo da kayayyaki musamman abinci da aka rubuta da harshen kasar Sin kawai ba tare da fassarar Turanci ba, lamarin da ya sabawa dokokin hukumar.

Ya ce dukkan kayayyakin da aka samu an kwace su, sannan an rufe wasu dakunan ajiya gaba daya tare da gayyatar masu su don karin bincike.

Hukumar NAFDAC ta yi gargadi ga ‘yan kasa da su kula da irin kayayyakin da suke saya da kuma amfani da su, domin a cewarta ba a tabbatar da inganci da lafiyar wadannan kayayyaki ba.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here