Hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Kano ta sanya ranar 8 ga Oktoba a matsayin wa’adi na biyan kashi 50 cikin 100 na kujerun Hajjin bana na shekarar 2026.
Daraktan hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Dan Baffa ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sulaiman Dederi, ya fitar a Kano.
Sanarwar ta ce wannan mataki na hukumar ya biyo bayan wata wasika da hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta aikewa jihohi, inda ta umarci kowace jiha da ta biya rabin kujerunta kafin ko zuwa wannan wa’adi.
“An bai wa Kano kujeru 5,684 domin aikin Hajji,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga masu niyyar zuwa Hajji da su hanzarta yin takardun kuɗin tafiya domin jihar ta samu damar cika kujerunta.
Hukumar ta kuma bayyana cewa ranar 31 ga Disamba za ta kasance wa’adi na ƙarshe na biyan kuɗin cikakken kudin Hajji.
A nasa jawabin, Shugaban hukumar, Alhaji Yusuf Lawan, ya roƙi taimakon Allah domin samun nasarar cika wannan umarni, tare da kira ga masu ruwa da tsaki da su ƙara jajircewa wajen cimma burin da aka sa gaba.
NAN