Mataimakin Gwamnan Kano ya taya ‘yan Najeriya murnar cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai

Aminu Abdussalam Gwarzo
Aminu Abdussalam Gwarzo

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya taya ‘yan Najeriya murnar cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai.

A cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ta hannun sakataren yada labaran sa, Ibrahim Garba Shuaibu, Gwarzo ya bayyana cewa bikin bukin lokaci ne na yin tunani kan tafiyar da kasar nan ta samu tun bayan samun ‘yancin kai da kuma nuna murnar nasarorin da ta samu.

Mataimakin gwamnan ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai domin ciyar da kasar gaba.

Gwarzo ya kuma yi amfani da damar wajen yin kira ga ‘yan Najeriya da su hada kai su rungumi zaman lafiya. Ya kara da cewa Najeriya za ta iya cimma burinta ne kawai idan ‘yan Najeriya suka hada kai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here