Kotun Tirabunal: Babu Kowa A Kujerar Gwamnan Kaduna – Isah Ashiru.

L R Uba Sani and Isah Ashiru

Dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Kaduna da aka yi ranar 18 ga watan Maris, Isah Ashiru, ya ce kujerar gwamnan Kaduna babu kowa.

Ashiru ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels TV’s cikin shirin siyasa a yau.

Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Kaduna a ranar Alhamis ta yi watsi da karar da Ashiru ya shigar a kan Gwamna Uba Sani, inda ta ce karar ba ta cancanta ba.

Sai dai hukuncin ya haifar da cece-kuce inda Sani da Ashiru kowanne ke ikrarin samun nasarar hukuncin.

Da aka tambaye shi wanene gwamnan jihar Kaduna bisa fassarar kotu, Ashiru ya ce, “A gare ni waccan kujerar babu kowa akanta ne bisa la’akari da cewa kotu ta bayar da umarnin a janye takardar shaidar cin zabe da INEC ta baiwa gwamnan.

“Gaskiyar magana ita ce an rantsar da shi a matsayin gwamna. Kotun ta ba da umarnin a janye takardar shaidarsa.”

Sai dai Ashiru ya yi kira ga magoya bayansa da su kasance masu yin addu’a da bin doka da oda, yana mai cewa zai daukaka kara kan hukuncin.

“Zan daukaka kara kan karar don tabbatar da cewa an dawo da burin mutanen mu. Mutanenmu masu bin doka ne. Za mu iya samun kujerarmu a Kotun Daukaka Kara, ya rage wa daya bangaren ya tunkari Kotun Koli ko a’a,” inji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here