‘Yan Najeriya sun yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan dakatar da kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC shiga yajin aikin da suka yi a fadin kasar, inda suka ce gwamnatinsa ta fi ta Muhammadu Buhari, wanda ya gabace shi.
Kungiyoyin NLC da TUC, a ranar Litinin, 5 ga watan Yuni, 2023, sun ce ba za su tsindima yajin aikin da suka shirya yi a fadin kasar nan a ranar Laraba ba.
Kudurin na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila; Shugaban NLC, Joe Ajaero; Shugaban TUC, Festus Osifo da Kachollom Daju, babban sakataren ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta tarayya.
An yanke shawarar ne bayan wata ganawa da gwamnatin tarayya ta yi da kungiyoyin kwadago a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
A cewar sanarwar bangarorin sun amince da cewa NLC za ta dakatar da sanarwar yajin aikin nan take domin samun damar tuntubar juna.
Janye tallafin man fetur PMS, an cimma matsaya kan cewa gwamnatin tarayya da TUC da kuma NLC za su kafa wani kwamitin hadin gwiwa da zai duba shawarar duk wani karin albashi da kuma kafa tsari da lokacin aiwatarwa.
“TUC da NLC za su ci gaba da yin cudanya da gwamnatin tarayya tare da tabbatar da samar da matsaya a kudurorin da ake takaddama.













































