Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Juma’a da Litinin 15 da 18 ga watan Aprilun 2022 a matsayin ranakun hutun Ester.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Ma’aikatar cikin gida ta tarayya Dakta Shuaib Belgore, ya fitar a madadin Ministan ma’aikatar, Ogbeni Rauf Aregbesola, wanda ya ayyana hutun a madadin Gwamnatin tarayya, ranar Talata a Abuja.
Ta cikin sanarwar Aregbesola ya bukaci Kiristoci dasu Kwaikwayi halayen Yesu, na sadaukarwa, da yafiya, da Hakuri da nuna Kauna ga Al’umma da kuma wanzar da zaman Lafiya.
Haka kuma ya yi kira ga ‘Yan Najeriya da su yi amfani da lokutan hutun wajen yiwa kasa addu’ar dawowar zaman Lafiya da kwanciyar hankali masu dorewa a wurin Allah Mai girma.
A karshe ya kuma yi fatan kiristoci zasu gudanar da bikin Ester din a gidajensu cikin kwanciyar hankali.













































