A yammacin yau Talata ne mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo, zai karɓi baƙuncin sanatocin jam’iyyar APC yayin buɗa bakin azumi.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata takardar gayyata da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisar, rTalata.
Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan Yahaya Abdullahi ne ya sanya wa wasikar hannu.
Ana sa ran gudanar da taron a gidan Aguda da isalin ƙarfe 6:30 na yamma.
A yammacin Lahadi da ta gabata ne Osinbajo ya karɓi baƙuncin gwamnonin jam’iyyar APC inda ya sanar da su burinsa na tsayawa takarar Shugaban ƙasa a 2023.
Haka kuma ana sa ran mataimakin shugaban ƙasar zai sanar da sanatocin jam’iyyar APC buƙatarsa ta neman ya gaji shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a lokacin buda baki.
Hakazalika mataimakin shugaban ƙasar zai gana da ƴaƴan jam’iyyar a majalisar wakilai a yammacin Laraba.
A cewar wata wasiƙa da mataimakin shugaban majalisar, Ahmed Wase ya karanta, Osinbajo ya ce, “A cikin wannan watan na Ramadan, zan yi matukar farin ciki da na karbi baƙuncin ku da ɗaukacin ƴaƴan jam’iyyar APC a Majalisar Wakilai ta tarayya zuwa buda baki a ranar Laraba, 13 ga Afrilu, 2022.”











































