A yau Talata ne mazauna garin Maiduguri suka gudanar da bikin saukar ruwan sama na farko a garin, inda suka bayyana jin dadinsu cewa zazzafan yanayin da suke fama da shi ya lafa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewa yankuna unguwannin Customs da New GRA da Abbaganaram da Polo da Damboa road har ma da Tashan Bama duk a cikin babban birnin jihar sun samu ruwa kamar da bakin kwarya tare da iska mai ƙarfi.
Rahotonni sun bayyana cewa, an fara ruwan Saman ne da misalin ƙarfe 2:40 na rana, kuma ya shafe fiye da mintuna 40.
An dai shafe kwanaki da dama ana matsanancin zafi wanda ya haura digiri 45 zuwa 47 a ma’aunin celcius.
Ismail Alfa, mazaunin New GRA, ya bayyana farin cikinsa da yadda ruwan sama ya kawo sauƙi ga tsananin zafi da ake fama da shi a watan Ramadan.
Alfa ya ce, “Gaskiya mutane da yawa ba su samu sauƙi a cikin kwanaki goma da suka wuce ba, suna azumi a Maiduguri, An tilasta wa mutane da yawa zama a gida yayin da wasu za su iya neman inuwa a ƙarƙashin bishiyoyi kawai don samun sauƙi, ”in ji shi.
Wani mazaunin garin Ali Goni ya bayyana cewa ruwan sama mai albarka ne da kuma annashuwa ga mazauna wannan birni.
Goni ya ce “Babu wanda ya yi tsammanin za a yi ruwan sama a wannan watan amma na ji dadi. Ina kashe akalla Naira 1000 a kullum don siyan ƙanƙara domin buɗa bakin azumin.
“Kuma saboda yanayin yana da zafi sosai, muna samun wahalar kwana a cikin gidajenmu, Yawancinmu muna kwana a waje,” inji shi.
Bashir Ahmed, wani mai tuƙa Keke Napep, ya ce zafin bana ba shi da sauƙi a gare mu wajen yin aiki a cikin rana mai zafi a Maiduguri, inda ya ce a wasu lokutan ya kan dakatar da wasu ayyukan saboda yana shan wahala.
“Wani lokaci, nakan tafi da sassafe kuma na tashi da misalin ƙarfe 11 na safe lokacin da rana ta yi zafi, Lallai wannan ruwan sama ya kawo mana sauƙi domin zafi ya ragu.” Inji shi.
NAN













































