Yanzu-yanzu: NAHCON ta kara wa’adin biyan kudin aikin hajjin 2024

NAHCON Chairman Jalal Arabi 750x430
NAHCON Chairman Jalal Arabi 750x430

← Back

Thank you for your response. ✨

 

Hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta kara wa’adin biyan kudin aikin hajjin shekarar 2024.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktan yada labaran hukumar Fatima Sanda Usara, ta fitar a ranar Talata.

Karanta wannan: Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira biliyan 100 kan shirin ciyar da ɗalibai

Sanarwar tace sabon wa’adin zai kare ne a ranar 31 ga watan Janairun 2024, maimakon 31 ga watan Disambar 2023.

Ta kara da cewa gwamnatin tarayya ta kara wa’adin ne domin bawa mutane damar yin aikin hajjin na bana.

Karanta wannan: Gwamnatin tarayya ta soke tantance takardun kammala Jami’o’in Benin da Togo

Sanarwar tace kara lokacin zai bada dama ga wadanda ba su biya kudin ba su biya suma a yi aikin hajjin da su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here