Shugaban karamar hukumar da aka yi garkuwa da shi a jihar Nasarawa ya shaki iskar yanci

Abdullahi Sule .jpg
Abdullahi Sule .jpg

Shugaban karamar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa Safiyanu Isah-Andaha, da yan bindiga suka yi garkuwa da shi ranar Litinin ya shaki iskar yanci.

Mai magana da yamun rundunar yan sandan jihar DSP Ramhan Nansel, ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin Labarai NAN ranar Talata a Lafiya.

Karanta wannan: NAHCON ta kara wa’adin biyan kudin aikin hajjin 2024

Yace haka kuma sun samu nasarar kubutar da wasu Karin mutum uku da suma aka yi garkuwa da su.

Tun a ranar Litinin ne aka yi garkuwa da shugaban karamar hukumar da karin wasu mutum 3 a kauyen Ningo dake karamar hukumar Akwanga.

Yace hadakar jami’an tsaro sun kubutar da shugaban karamar hukumar da sauran mutane 3 da misalin karfe 8:45 na daren Talata a kauyen Andaha, dake karamar hukumar Akwanga.

Ya kara da cewa babu wani kudin fansa da aka biya kafin sakin shugaban karamar hukumar da sauran mutane 3n da aka yi garkuwa da su.

Sai dai bayanai da aka tattaro sun nuna cewa sai da aka biya naira miliyan 10 Kafin sakin shugaban karamar hukumar, bayan da yan bindigar suka nemi a basu miliyan 50.

Nansel yace yanzu haka wadanda suka kubutar ana duba lafiyar su kuma da zarar an kammala za a sada su da iyalan su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here