Yadda ‘yan ta’adda suka kai wa ayarin motoci na hari – Mataimakin Gwamnan Kebbi 

Yombe
Yombe

Mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Samaila Yombe da ya tsallake rijiya da baya, ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun yi kama da al’umma, wanda hakan ya sa Jami’an tsaro suka kasa gane su.

Da yake bayyana halin da ya shiga da manema labarai a yammacin ranar Laraba, Yombe, wanda tsohon Kanar mai ritaya ne a aikin soja, ya ce ya je kauyen Kanya da ke Masarautar Zuru ranar Talata tare da kwamandan Bataliya ta 223.

Ya ce manufarsa ita ce tantance irin tallafin da gwamnatin jihar ke baiwa hukumomin tsaro a jihar.

Yombe ya ce a lokacin da ayarinsa suka isa kauyen sun samu rahoton tsaro cewa ‘yan bindigar sun riga sun hade da jama’ar gari.

“Lokacin da muka isa Kanya a ranar Talata, mun samu rahoton cewa ‘yan bindigar sun saje da mazauna Kanya.

“Don haka, da wuya a yi yaƙi da ‘yan bindigar a tsakiyar jama’a, saboda idan aka yi haka barnar da za’a yi zata yi yawa.

“Sai kuma muka dauki dabarar ficewa daga garin domin su biyo mu. A cikin wannan tsari, saboda mun kasance masu rauni, duka bangarorin biyu sun sami asarar rayuka.

Ya kara da cewa, “daga harbin bindiga, za ka dauka ‘yan ta’adda 200 ko 250 ne.

Kuma sojojin runduna ce ta dakaru kusan 30, wadanda suka yi wa babban kwamandan rakiya.

“Ta bangaren karfi, sojoji sun cika da yawa. Ba abu ne mai yiyuwa sojojin su yi motsi ba amma sun sami damar ficewa daga ‘yan ta’adda zuwa kasa wani waje.

” Sai dai da aka nemi ya bayyana adadin wadanda suka mutu a bangaren gwamnati, sai ya ki ya ce, “A’a, ba zan iya bayyana adadin ba. Hakan ya saba wa ka’idojin aiki”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here