Sakataren APC ya mayar wa Wike martani, ya bukace shi da ya yi murabus ya fuskanci siyasar jihar Rivers

Wike and Senator Bashiru 750x430

Sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ya gargadi Ministan Babban Birnin Tarayya FCT, Nyesom Wike, da ya daina abin da ya bayyana a matsayin yunkurin dagula jam’iyyar mai mulki, yana mai cewa ya dace ministan ya yi murabus daga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu idan ba zai iya dakatar da tsoma baki a harkokin jam’iyyar ba.

Basiru ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai tsauri da ya fitar a Abuja, inda ya ce hankalinsa ya koma kan kalaman da ya bayyana a matsayin hare-hare daga Ministan FCT a kansa da kuma ofishinsa na sakataren APC na ƙasa, bayan ya tsaya kan cewa dukkan mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa dole su girmama kowane gwamna mai ci, domin gwamnonin su ne shugabannin jam’iyyar a jihohinsu.

Ya bayyana mamakinsa kan yadda wata magana da ya ce ba ta da wata illa ta janyo martani mai tsauri daga wani mamba na majalisar zartarwa ta tarayya, yana mai cewa bai dace Wike ya ci gaba da zama a cikin gwamnatin APC yayin da ake zarginsa da haddasa rikice-rikice a cikin jam’iyyar ba.

Basiru ya kara da cewa Wike ba shi da hurumin tsoma baki a harkokin cikin gida na APC, domin a bayanan jam’iyyar sun nuna Wike ba mamba ba ne na APC, don haka ba shi da ikon shiga al’amuran jam’iyyar.

Ya kuma ce a matsayinsa na sakataren jam’iyya na ƙasa, yana da alhakin kula da harkokin APC a duk fadin ƙasar, ba a Jihar Osun kawai ba.

Labari mai alaƙa: Rikicin jihar Rivers: Wike ya yi barazanar  daukan mataki a kan sakataren APC na ƙasa, Basiru

Ya kuma karyata zargin da ke alakanta shi da sha’awar kudaden Jihar Rivers, yana mai cewa irin wadannan zarge-zarge ba su da tushe kuma ba su dace da tarihin aikinsa ba, kuma ya shahara da rikon amana da tsayawa kan ka’ida tun daga gwagwarmayar yaki da mulkin soja.

A baya, Nyesom Wike ya gargadi Basiru da ya nisanci siyasar Jihar Rivers, yana mai cewa wasu ’yan siyasa suna anfani da jita-jitar kudade a baitulmalin jihar suna yin maganganu marasa tushe.

Wannan gargadi ya biyo bayan kalaman da aka danganta ga wasu jiga-jigan APC da suka nuna rashin girmamawa ga Gwamna Siminalayi Fubara, lamarin da Basiru ya bayyana a matsayin abin takaici tare da jaddada bukatar girmama mukamin gwamna.

Basiru, a martaninsa na karshe, ya ce a matsayinsa na sakataren APC na ƙasa, yana da alhakin kare muradun jam’iyya da tsarinta, yana mai cewa goyon bayan da Wike ke nunawa Shugaba Bola Tinubu ba yana nufin ya zama mamba na APC ba.

Ya gargadi cewa duk wani yunkuri na dagula APC a Jihar Rivers ba za a lamunta ba, kuma ba zai bari a shigo da salon PDP cikin APC ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here