Gwamnatin tarayya ta fito da sabbin dabaru na daƙile maguɗin jarabawa

Morufu Tunji Alausa 678x430

Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da sabbin dabaru da nufin daƙile maguɗin jarabawa a Hukumar Jarabawar Afirka ta Yamma WAEC da Hukumar Jarabawar Ƙasa NECO  daga shekarar 2026, a wani ɓangare na ƙoƙarin dawo da sahihanci da amincewar jama’a ga tsarin tantance ilimi a Nijeriya.

Ministan ilimi, Dakta Morufu-Tunji Alausa, tare da ƙaramin ministar ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmed, sun bayyana matakan a birnin Abuja, inda suka jaddada cewa an tsara sauye-sauyen ne domin ƙarfafa gaskiya da tsaurara sa ido a dukkan matakan gudanar da jarabawar ƙasa.

Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta nuna ƙudurin magance matsalolin da suka daɗe suna addabar jarabawar gwamnati, musamman maguɗi da sauran kura-kuran da ke rage amincewa da sakamakon jarabawa a faɗin ƙasar.

Karanta: Gwamnatin tarayya ta kafa cibiyoyin koyarwa 119 domin inganta ilimin Almajirai

A cikin manyan matakan da aka shimfiɗa, ma’aikatar za ta yi amfani da fasahar zamani tare da tsauraran dokoki na gudanarwa domin kare sahihancin jarabawar WAEC da NECO, ciki har da ingantaccen tsarin bazuwar tambayoyi da bambance tsarin su daga ɗalibi zuwa ɗalibi.

Ko da yake ɗalibai za su amsa tambayoyi iri ɗaya, sai dai tsarin jerin tambayoyin da yadda aka gabatar da su za su bambanta tsakanin ɗalibi da ɗalibi, matakin da ma’aikatar ta bayyana cewa zai rage haɗin baki da maguɗi a ɗakunan jarabawa.

Gwamnatin tarayya ta kuma sake jaddada matsayarta kan sauya makaranta a matakin ajin kammala sakandare, inda ta nuna cewa dokar hana canjawa ɗalibai makaranta a wannan mataki za a fara aiwatar da ita ba tare da sassauci ba, domin hana sauye-sauyen da ake danganta su da maguɗin jarabawa.

Baya ga haka, an amince da sabbin ƙa’idojin ƙasa kan tantancewar ci gaba ta ɗalibai, tare da wajabta wa dukkan hukumomin jarabawa bin lokutan miƙa bayanan tantancewa, sannan a ƙaddamar da lambar tantance ɗalibi ta musamman domin ƙarfafa sa ido, alhaki da inganta tsarin jarabawa a faɗin Nijeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here