Dan uwan Kwankwaso ya maka Gwamna Yusuf a Kotu kan rikicin fili

Abba Kabir Yusuf 750x430
Abba Kabir Yusuf 750x430

Wata sabuwar takaddama ta kunno kai tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da dan uwan Kwankwaso, Garba Musa Kwankwaso, game da batun raba fili a birnin Kwankwasiyya na Kano.

Karar da Garba ya shigar ta ta’allaka ne kan wani katafaren fili da aka baiwa WAECO Nigeria Limited tun farko a zamanin gwamnatin tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso.

Takardun kotun sun bayyana cewa wadanda ake tuhumar sun hada da kwamishinan filaye da tsare-tsare na jihar, hukumar tsare-tsare da raya birane ta jihar Kano (KNUPDA), babban lauyan gwamnatin jihar Kano, da sauran su.

Garba Kwankwaso ya nemi a ba shi damar shiga tsakani domin hana gwamna da sauran jam’iyyu daukar duk wani mataki da ake ganin ya saba wa muradun sa game da filin.

Rikicin filaye ya samo asali ne tun a shekarar 2017 da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta gudanar, inda ta nuna cewa WAECO, kamfanin da aka bawa filin, ba hukuma ba ce da shari’a ta samar a lokacin rabon.

Hukumar ta gano cewa Rabiu Kwankwaso da dan uwansa su ne suka kasance daraktoci a kamfanin.

A bisa wannan binciken ne hukumar ta bayar da shawarar a soke kason da aka ware, wanda hakan ya sa gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ta sake yin hasafin wajen.

A lokacin Gwamna Ganduje, an ware wasu kaso na filin ga dandalin Mallam Kato da sauran masu asali, ciki har da dangin Dantata.

Sai dai majiyoyi na zargin cewa Gwamna Yusuf ya bijirewa kwace filin tare da mayar da shi ga kamfanin WAECO Nigeria Limited wanda hakan ya sa Garba Kwankwaso ya dauki matakin shari’a ta hanyar maka shi a kotu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here