APC ta bayyana ranar da za ta gudanar da taron majalisar zartaswa na jam’iyyar 

APC
APC

Jam’iyyar APC ta tsayar da ranar Alhamis 17 ga watan Maris 2022 a matsayin ranar gudanar da taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar na kasa (NEC).

Wata sanarwa da Salisu Na’inna Dambatta Daraktan yada labarai na hedikwatar jam’iyyar APC ta kasa, Abuja ya fitar a ranar Alhamis, ta tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarsa, sanarwar taron ta samu sanya hannun mambobin kwamitin riko na jam’iyyar.

“Bisa ga sashi na 25B (i da ii) na Kundin Tsarin Mulkin Jam’iyyar, da kuma ikon da aka baiwa Kwamitin riko ta cikin kudurin NEC na ranar 8 ga Disamba, 2020, kwamitin riko na Jam’iyyar zai gudanar da taron majalisar zartaswa karo na 23, A ranar 8 ga Maris, 2022, don duba al’amuran da suka shafi babban taron kasa, gudanar da mulkin jam’iyyar da duk wani abin da ya dace. jam’iyyar.”

Sanarwar ta ce za a gudanar da taron ne da misalin karfe 11 na safe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here