Darakta Janar na Hukumar Kula da Matasa masu hidimar Kasa, Manjo Janar Shu’aibu Ibrahim, ya shawarci masu hidimar da su yi watsi da sakonnin da masu aikata laifuka ta intanet ke yadawa dangane da biyan kudi domin kai su wuraren aiki masu kyau
Wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na NYSC, Emeka Mgbemema ya fitar ta ce shugaban ya bayar da wannan shawarar ne a ranar Laraba a lokacin da yake jawabi ga Rukunin A kashi na farko na shekarar 2022 a sansanin masu hidimar kasa na Yakubu Gowon dake Fanisau, jihar Jigawa.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa, kai mutane wurin aiki da kuma sauya musu gari kyauta ne, don haka su guji biyan kowa kudi saboda wadannan dalilai.
“Babban Darakta ya kuma yi gargadin cewa laifi ne a gabatar da rahotannin likitanci na bogi da nufin samun samun sauyin gari, inda ya ce duk wanda aka kama yana yin haka zai fuskanci fushin doka,” in ji sanarwar.
“Ya kuma yi tir da halin da wasu matasan da ke da muggan cututtuka ke boye yanayin su wajen yin rajistar shiga aikin yi wa kasa hidima.
“Shugaban ya kuma umarce su da su ci gaba da isar da saƙon zaman lafiya da haɗin kai a duk inda suka sami kansu.”
“Ibrahim ya shawarce su da su sanya kishin kasa, gaskiya da aiki tukuru, yana mai jaddada cewa ya kamata su mai da hankali kan burinsu.”













































