Daliban sakandire 6 sun nutse a kogi bayan dawowa daga jarrabawa a Kaduna

kogi, Daliban, sakandire, nutse, dawowa, jarrabawa, Kaduna
Daliban makarantar sakandare shida sun nutse a kogin Mbang da ke kauyen Ribang (Mbang) a karamar hukumar Kauru na jihar Kaduna.Matasan, a cewar rahoton sun...

Daliban makarantar sakandare shida sun nutse a kogin Mbang da ke kauyen Ribang (Mbang) a karamar hukumar Kauru na jihar Kaduna.

Matasan, a cewar rahoton sun nutse ne a lokacin da suke dawowa daga jarrabawar WAEC da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Talata.

Wadanda lamarin ya shafa sun hada da Manasseh Monday mai shekaru 16 da Mausa John mai shekaru 16 sai Pius David mai shekaru 15 da kuma Monday Ayuba mai shekaru 16 tare da David Danlami mai shekaru 19 da Yahuza Audu mai shekaru 16.

Karin labari: Yanzu-yanzu: El-Rufa’i ya maka majalisar dokokin jihar Kaduna a Kotu

Jami’in hulda da jama’a na kungiyar raya Ribang na kasa Fasto Simon Ishaku, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Larabar da ta gabata, ya bayyana cewa cikin alhini tuni aka gano gawarwaki uku tare da binne su.

Ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, akwai sauran guda uku da aka gaza gano inda suke a kogin.

“Yaran sun bar gidajensu ne cikin koshin lafiya da annashuwa bayan iyayensu sun tafi gona, inda su kuma daliban suka tafi rubuta jarrabawa a ranar, kwatsam sai suka gamu da iftila’in.

Karin labari: ‘Yan sanda sun kama mai sana’ar POS kan zargin kawalci ga ‘yan fashi

“Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da Gwamna Uba Sani da Sanata Sunday Katung da ‘yan Majalisar Wakilai da su taimaka mana da makarantu da asibitoci da hanyoyin shiga da gada domin kawowa al’ummarmu taimako” in ji Simon.

Saidai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, bai amsa kira da sakon karta kwana da manema labarai suka aike masa har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here