Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najriya ta kammala shirin fara jigilar dare kafin rubu’I na biyu na wannan shekarar ta 2024.
Manajan daraktan hukumar Fidet Okhiria, ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, a ranar Litinin.
Karanta wannan: Shugaban karamar hukumar da aka yi garkuwa da shi a jihar Nasarawa ya shaki iskar yanci
Yace “Abinda ya rage mana yanzu shi ne fara jigilar dare, domin ana bukatar ace ko da yaushe ana jiragen kasa na yin jigila. Mutane da dama suna son yin tafiy-tafiye da yamma, amma saboda matsalar tsaro dake addabar kasar nan ya sanya muka takaita zirga-zirgar mu kawai ido na gani ido.
Karanta wannan: NAHCON ta kara wa’adin biyan kudin aikin hajjin 2024
A cewarsa, da zarar an fara jigilar daren hakan na nufin za’a rinka lodi sau 6 a ko wacce rana.
Yace “ Zamu kara adadin jiragen da za su rinka jigalar fasinja daga Legas zuwa Ibadan, ko daga Warri Itakpe da kuma Abuja zuwa Kaduna, wanda hakan na nufin sau 3 jiragen za su rinka zuwa su dawo sau 3, da hakan ya sanya idan aka yi jimillar su sun zama sau 6 kenan a kowacce rana.