Hukumar ICPC ta fara gudanar da bincike kan zargin kammala digiri cikin mako 6 a Benin

ICPC Operatives
ICPC Operatives

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC, ta ce ta fara bincike kan zargin samun shaidar karatun digiri ba bisa ka’ida ba a jami’ar Cotonou da ke jamhuriyar Benin.

The anti-graft agency has also called upon stakeholders in government and in the education sector to join hands in finding a solution to the alleged fraud.

Ta kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a bangaren gwamnati da kuma bangaren ilimi da su bada hadin kai domin samun matsaya game da zargin.

Karanta Wannan: Hukumar kula da zirga-zirgar jiargen Kasa za ta fara Jigilar dare

A wata sanarwa da mai Magana da yawun hukumar Azuka Ogugua, ya fitar, ta bayyana cewa shugaban hukumar Dakta Musa Adamu Aliyu, SAN, ya kira wani taro a kan batun, a ranar Talata.

Binciken zai shafi jami’ar Ecole Superieure de Gestion et de Technologies (ESGT) ta Cotonou wadda ake zargin tana bayar da shaidar digiri a kasa da mako shida.

Karanta wannan: Shugaban karamar hukumar da aka yi garkuwa da shi a jihar Nasarawa ya shaki iskar yanci

Hukumar ta ce za ta yi binciken don gano hanyoyin da ake bi domin yin badakalar da zummar kawo gyara a tsarin karatun.

Sannan za ta yi hadin guiwa da hukumomi na cikin gida da na waje domin tabbatar da ingancin shaidar karatun tare da zakulo wadanda ke da hannu a al’amarin.

Karanta wannan: Gwamnatin tarayya ta soke tantance takardun kammala Jami’o’in Benin da Togo

Rahotan da ya bankado hakan ya yi zargin cewa ana samun kwalin karatun ba tare da bin hanyoyin da suka dace ba, kamar rashin gabatar da takardar bukatar yin karatu da rijista da karatun da kuma rashin rubuta jarrabawa.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin Najeriyar ta sanar da dakatar da karbar shaidar digiri daga Cotonou da kuma Togo sakamakon badakalar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here