Kotu ta dage gurfanar da Sowore kan zargin aikata laifuka ta internet

sowore2

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ƙarƙashin mai shari’a Mohammed Umar ta dage gurfanar da ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan Adam, Omoyele Sowore, zuwa ranar 27 ga Oktoba, 2025.

A zaman da aka shirya a ranar Talata, an fasa fara gurfanar da shi ne saboda ba a kai masa takardun ƙarar tuhumar zargin laifin amfani da intanet ba, waɗanda suka ƙunshi ƙara guda biyar.

Daraktan gurfanar da masu laifi daga ma’aikatar shari’a ta tarayya ya bayyana wa kotu cewa gwamnatin tarayya da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun shirya gurfanar da Sowore tare da kamfanonin sada zumunta, X da Meta (Facebook), a matsayin waɗanda ake tuhuma na farko zuwa na uku.

Sai dai lauyan Sowore, Marshal Abubakar, ya sanar da kotu cewa ba a miƙa musu takardun ƙarar ba.

Lauyan da ke kare kamfanin Meta ya goyi bayan wannan batu, yana mai cewa shi ma a cikin kotu aka bashi takarda a karo na farko.

Duk da haka, wanda ake tuhuma na biyu bai samu lauya da zai wakilce shi ba a ranar.

Labari mai alaƙa: Sowore ya kai ƙarar DSS, Meta da X bisa zargin take masa haƙƙin ɗan adam

Rahotanni sun ce laifin da ake zargin Sowore da shi shi ne wallafa wani rubutu a shafin sa na X a ranar 25 ga Agusta, wanda gwamnatin tarayya ta bayyana da cewa ya sabawa sashe na 24(2)(b) na dokar hana laifukan internet ta 2024.

A baya dai, hukumar DSS ta bai wa Sowore wa’adin mako guda a ranar 8 ga Satumba da ya goge abin da ta kira da “rubutu na ƙarya, da cin mutunci da tayar da hankali” kan shugaban ƙasa Bola Tinubu, wanda kuma wa’adin ya ƙare a ranar 15 ga Satumba ba tare da ya goge rubutun ba.

Sai dai a martani, Sowore ya shigar da ƙara guda biyu a babbar kotun tarayya, Abuja, yana kalubalantar DSS da kamfanonin sada zumunta Meta da X.

Lauyansa, Tope Temokun, ya bayyana cewa ƙarar ta shafi batun “rayuwar ’yancin faɗar albarkacin baki a Najeriya,” yana mai jaddada cewa idan aka ba hukumomin gwamnati damar umartar kamfanonin duniya su rufe baki ga ’yan ƙasa, to babu wani ɗan Najeriya da zai kasance cikin tsaro.

Kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 27 ga Oktoba, 2025, domin ci gaba da sauraron ƙarar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here