zaben Osun: INEC ta bawa Ademola Adeleke takardar shaidar nasarar cin zabe

adeleke ademolaa 680x375 1 1
adeleke ademolaa 680x375 1 1

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta mika takardar shaidan nasarar cin zaɓe ga Ademola Adeleke, zabebben gwamnan Jihar Osun kuma ɗan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Adeleke, dan takarar gwamnan na jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya lallasa abokin hamayyarsa kuma gwamna mai ci Gboyega Oyetola inda ya samu kuri’u 403,371 , A Zaben gwamnan Osun a shekarar 2018, an fafata tsakanin Adeleke da Oyetola amma a wancan lokacin dan takarar ba APC ya yi nasara bayan an yi zaben raba gardama.

Adeleke ya samu kuri’u 403,371 inda ya doke Gboyega Oyetola, gwamnan Osun kuma ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Congress APC a zaben na gwamna.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here