Jam’iyyar APC da dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu a hukumance sun kaddamar da Sanata Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023.
An gudanar da bikin kaddamar da Shettima ne a dakin taro na Shehu Musa Yar’adua da ke Abuja, a yau Laraba, 20 ga watan Yuli.
Bikin ya samu halartar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu da Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti.
Hakazalika, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi da Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno da Gwamna Abdullahi Ganduje Jihar Kano duk sun hallarci taron.
Sauran wadanda suka halarci bukin kaddamarwar sun hada da Iyiola Omisore, sakataren jam’iyyar APC na kasa, da wasu manyan manyan baki.













































