Rikicin APC Kano: Bangaren Shekarau sun bukaci a basu kaso 55 na tsarin shugabancin jam’iyyar

EA0DF583 49AD 41C9 9F22 1A7A9351EFDE
EA0DF583 49AD 41C9 9F22 1A7A9351EFDE

Kudirin sulhu na rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar APC a Kano da alama yana kara samun koma baya ganin yadda bangaren  Sanata Ibrahim Shekarau ta dage cewa dole ne a tabbatar da adalci ga duk ‘ya’yan jam’iyyar.

Bangaren bayan wata wasika da bangaren suka aike wa hedikwatar jam’iyyar ta kasa a ranar 7 ga watan Fabrairu na kin amincewa da tsarin raba jam’iyyar da aka fitar na Kano, yanzu haka bangaren na sanata Shekarau sun kara  mika wata wasika zuwa hedikwatar jam’iyyar APC mai dauke da kwanan watan 10 ga Fabrairu, 2022.

A cikin wasikar, sun bukaci kashi 55 na tsarin shugabancin jam’iyyar , sannan kuma dole ne  shugaban jam’iyyar ya fito daga bangarensu.

Solacebase ta rahoto cewa wadanda suka sa hannu kan takararar sune: Sanata Ibrahim Shekarau (Sanatan Kano ta tsakiya), Sanata Barau Jibrin (Sanatan Kano ta Arewa), Tijjani Jobe (Dan majalisar tarayya mai wakiltar D/Tofa/Rimingado), Nasiru Gabasawa (Dan majalisar tarayya mai wakiltar Gezawa/Gabasawa), Haruna Dederi (Dan majalisar tarayya mai wakiltar Karaye/Rogo), Sha’aban Sharada (Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal) da Shehu Dalhatu (Shugaban kungiyar goyon bayan Buhari).

Sun kuma dage kan cewa ba su yadda gwamna Ganduje ya jagoranci kwamitin sulhu ba domin yana daga cikin rigimar.

Hakazalika, a cikin wasikar, a matsayin wani bangare na ci gaba da sasantawar, ta bukaci a janye dukkan kararrakin da bangaren Gwamna ya shigar a matsayin shaida na tsari na gaskiya da zai iya karfafa kwarin gwiwarmu.

Wasikar ta karanta a wani bangare: “Muna kan samun wasiƙarku mai kwanan wata 8 ga Fabrairu, 2022 game da batun da aka ambata a sama, wanda aka yi wa shugabanmu, H.E. Dist. Sanata Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano) a ranar 9 ga Fabrairu 2022, kuma a matsayin martani, muna rubuto muku.

Wasikar ta jaddada bukatu 3 da bangaren G7 suke bukatar a aiwatar domin tabbatar da sulhun.

“1. Har yanzu muna tsaye kan kudurinmu na kashi 55%, sannan Shugaban jam’iyya na Jiha ya kasance daga bangaren mu. Mun amince mu bawa gwamna  kashi 45% na mukaman jam’iyya, ba tare da wata tangarda ba.

“2. Duk wani kwamitin sulhu da za’a yi to kada ya kasance karkashin gwamnata Ganduje, saboda shima yana cikin rigimar.

“3. Kafin a Ci gaba da aiwatar da sulhu dole ne ya kasance bangaren gwamna sub janye duk wasu ƙararrakin da suka shigar, wanda haka zai sa mu tabbatar da gaske suke.

“Muna kira gare ku, da ku zurfafa bincike a kan kura-kuran da ke cikin babbar jam’iyyarmu ta Jihar Kano, kuma ku yi duk abin da ya dace ta hanyar bin doka da oda, don kwato jam’iyyar daga mawuyacin halin da take ciki.

“Kamar yadda aka saba, muna addu’ar Allah ya yi shiriya da kariya a gare ku a cikin ayyukanku.” inji Wasikar da bangaren Sanata Shekaru suka aikewa uwar jam’iyyar APC ta kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here