‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ‘yan sandan Jihar Nasarawa 10, a kan hanyar su ta dawo wa daga zaben Osun

BANDITS 1
BANDITS 1

‘Yan bindiga sunyi garkuwa da jami’an ‘yan sandan jihar Nasarawa 10, akan hanyar su ta dawo wa daga zaben Osun.

Wani jami’in ‘yan sanada ya bayyana cewa anyi garkuwa da ‘yan sandan ne a jihar Kogi, ranar 17 ga watan da muke ciki, a kan hanyar su ta dawo daga Osun.

“Ranar 17 ga watan da muke ciki, da misalin karfe 11:05 a ofishin ‘yan sanda na Obajana, muka samu labarin cewa an ji karar bindiga a Obajana.”

“Hakan yasa DPO ya tura jami’an ‘yan sanda don bin sahun karar bindigar, amma koda suka isa gurin sun tarar da mota mai cin mutane 18 a gurin, tare da mutane bakwai, inda suka bayyana kansu a matsayin jami’an ‘yan sanda, kuma sun dawo daga zaben Osun ne.”

“Amma a halin yanzu an tura jami’an tsaro dun bin sahun masu garkuwar, tare da tsiratar da wanda akai garkuwar dasu.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here