Gwamnatin Tarayya ta amince da Naira Biliyan 32.9 domin faɗaɗa aikin samar da kulawar lafiya ta matakin farko a faɗin ƙasa

IMG 20251219 WA0067 750x430

Gwamnatin tarayya ta amince da sakin Naira Biliyan 32.9 ƙarƙashin asusun kula da lafiyar a matakin farko na ƙasa domin zango na huɗu na shekarar 2025, tare da tsara fara rabawa jihohi da hukumomin da abin ya shafa daga farkon shekarar 2026.

An bayyana wannan ne a taron sa-ido na ministoci na ƙasa karo na goma sha uku kan asusun kula da lafiyar a matakin farko da aka gudanar a Abuja, wanda ya mayar da hankali kan duba cigaban aiwatar da shawarwarin da aka yanke a baya da kuma ƙarfafa gaskiya da ɗaukar alhaki a sabon tsarin asusun.

Ministan lafiya da walwalar jama’a Farfesa . Muhammad Ali Pate ya bayyana cewa amincewar ta nuna ƙudurin gwamnatin tarayya na ƙarfafa isar da kulawar lafiya ta matakin farko ta hanyar tsarin kuɗi mai tabbaci, bayyananne kuma abin dogaro.

Ya ce rabon kuɗin ya yi daidai da sabon tsarin asusun na zamani, domin tabbatar da cewa cibiyoyin lafiya na matakin farko sun samu isasshen kuɗi da ingantaccen kulawa.

Ya kuma jaddada cewa manufar ba wai kashe kuɗi kawai ba ce, sai dai ganin sakamako mai amfani ga jama’a, musamman uwa da yara da al’umma gaba ɗaya.

A cewarsa, an tsara shirin ne yadda albarkatu za su isa kai tsaye wuraren aiki su koma hidima ta ainihi.

A wani mataki na ƙarfafa mallakar shirye-shiryen a matakin ƙasa, kwamitin ya amince da faɗaɗa mambobinsa ta hanyar shigar da ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta ƙasa.

A cewar su, wannan zai ƙara sa hannun ƙananan hukumomi, ɗaukar alhaki da mallakar shirin, ganin cewa yawancin ayyukan kulawar lafiya ta matakin farko ana aiwatar da su ne a wannan mataki.

Taron ya kuma amince da kafa cibiyar martanin ‘yan ƙasa domin ƙarfafa gaskiya da sa ido daga ɓangaren jama’a a fannin lafiya.

Cibiyar za ta bai wa ‘yan ƙasa damar yin tambayoyi, gabatar da ƙorafe-ƙorafe da bayar da ra’ayi kan ayyukan lafiya da ake tallafa wa, domin a rika gyara inda ake buƙata.

Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa wannan asusun kula da lafiyar a matakin farko wanda aka kafa ta dokar lafiya ta ƙasa, shi ne ginshiƙin tsarin kuɗin kula da lafiyar matakin farko domin tabbatar da ɗorewar kuɗi da kuma inganta samun muhimman ayyukan lafiya, musamman ga talakawa da masu rauni a duk faɗin ƙasar nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here