Ba mu cancanci haka ba, mun yi maka kamfen, ka tabbatar an yi wa mijina adalci – Matar El-Rufai ta shaida wa Tinubu

WhatsApp Image 2026 07 07 at 9.30.50 PM 1783457568 750x430

Hajiya Asia El-Rufai, matar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, a ranar Talata ta roki Shugaba Bola Tinubu da ya tabbatar an yi wa mijinta adalci, tana mai cewa ana wahalar da su duk da goyon bayan da suka ba Shugaban kasa a lokacin yakin neman zaben 2023.

Asia, wadda ta yi magana tare da matar El-Rufai Aichatou, a gidansu dake Abuja, ta ce iyalinta basa neman Shugaban kasa ya shiga cikin shari’ar da ke gudana, sai dai su na son a tabbatar tsohon gwamnan ya samu ‘yancin shin a dan kasa da kundin tsarin mulki ya ba kowane dan Najeriya.

Rokon na ta ya zo ne sa’o’i kadan bayan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ICPC ta tabbatar da kama likitan El-Rufai na musamman, Farfesa Bello Abubakar, bisa zargin bada bayanan karya da suka shafi ziyarar likita ta tsohon gwamnan yayin da yake tsare.

Asia ta kuma yi zargin cewa mijinta, wanda ta ce an gano yana da matsalar hawan jini da ciwon siga, an hana shi samun isasshen magani.

Ta bayyana irin rawar da ita da mijinta suka bayar a lokacin yakin neman zaben shugaban kasa Tinubu.

“Mai girma Shugaba kasa, na yi kamfen saboda kai. Na tashi na zagaya ko ina a Jihar Kaduna domin kai. Mijina ya tsaya tare da kai. Shin wannan ne abin da iyalinmu suka cancanta?
“Kwallo tana hannunka, Shugaba kasa, duk wannan zai iya tsayawa idan ka ce kalma daya kawai, mun yi imani kai uba ne, kuma mun san zaka iya tausayawa,” in ji ta.

Asia ta jaddada cewa iyalin ba sa neman wani fifiko na musamman ko shigar siyasa cikin tsarin shari’a.

“Don Allah, ba na rokonka ka ce kada su gurfanar da shi, amma muna rokonka ka bari ya samu ‘yancin dan adam da kundin tsarin mulkin da ka rantsu zaka kare.
“Ka bari su bada shi beli da zai iya cikawa. Idan ya aikata laifi, a bari kotu ta yanke hukunci. Idan bai yi ba, shima kotu ta yanke hukunci.”

Ta yi zargin cewa ci gaba da tsare El-Rufai da kuma hana shi ganawa da likitoci, ‘yan uwa da lauyoyi ya sa iyalinsa cikin tsananin damuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here