Shugaba Biden ya yi Allah wadai da kakkausar suka kan kalaman da magabacinsa Donald Trump ya yi cewa zai ƙarfafa gwiwar Rasha wajan kai wa ƙasashen ƙungiyar tsaro ta Nato hari wadanda ba sa biyan kudi masu yawa a harkar tsaro.
Karanta wannan: Kotu ta daure Aisha Alkali Wakil kan laifin damfarar Naira Miliyan 40
Mista Biden din ya yi tur da kalaman da tsohon shugaban kasar Amurka ya yi a wani gangamin yakin neman zabe inda ya bayyana su a matasyin abun kunya da hadari da suka yi hannun riga da halayyar Amurkawa.
Shugaba Biden ya yi wannan maganar bayan da majalisar dattijan kasar ta amince da wani gagarumin tallafin soji ga kasar Ukraine.