Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP ya dakatar da Sule Lamido, wanda yake daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar, bisa zarginsa da halartar tarurrukan da ba su halatta ba, waɗanda ke barazana ga haɗin kai, kwanciyar hankali da mutuncin jam’iyyar.
Kwamitin ya kuma tabbatar da sahihancin babban taron jam’iyyar na baya-bayan nan tare da nuna cikakken goyon baya ga shugabancin kwamitin gudanarwa na ƙasa ƙarƙashin Kabiru Tanimu Turaki.
Baya ga Lamido, kwamitin ya kuma dakatar da tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, tare da wasu mutum shida bisa laifuka iri ɗaya.
Sauran da aka dakatar sun haɗa da Maxwell Okudoh daga Anambra, Jones Onyereri daga Imo, Chinwe Onuorah daga Anambra, Otuekong Emmanuel Ibiok daga Akwa Ibom, Effiok Cobha daga Cross River da Philp Salawu daga Kogi.
Shugaban kwamitin ya bayyana cewa an mika dukkan waɗanda aka dakatar zuwa ga kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar domin ci gaba da ɗaukar matakan ladabtarwa da suka dace da dokokin jam’iyyar.
Wannan bayani ya fito ne a cikin sanarwar da kwamitin ya fitar bayan taron da ya gudanar a ranar Laraba, wadda shugaban kwamitin, Sanata Adolphus Wabara, ya fitar a ranar Juma’a.
Sanarwar ta nuna cewa kwamitin ya duba ci gaba da halartar wasu mambobinsa tarurrukan da ba su dace ba, tare da yanke shawarar dakatar da su daga dukkan ayyukan kwamitin amintattu.
Kwamitin ya kuma yi kira ga INEC da ta sabunta shafinta ba tare da ɓata lokaci ba domin nuna sauyin shugabanci a jam’iyyar sakamakon babban taron ƙasa da kuma karewar wa’adin tsohon kwamitin gudanarwa na ƙasa.
Haka kuma, kwamitin ya buƙaci dukkan mambobin PDP da su rungumi haɗin kai, su dakatar da saɓani, su koma tsagin jam’iyyar domin gina ƙarfi ɗaya da zai kuɓutar da ƙasa daga abin da ya bayyana a matsayin danniya da mulkin APC.
Kwamitin ya nuna kwarin gwiwar cewa ƙararorin shari’a da ke gudana kan jam’iyyar za su ƙare da nasara, tare da fitowar PDP a matsayin jam’iyya mafi ƙarfi da haɗin kai.
Kwamitin ya jaddada cewa ƙarfin PDP ba ya dogara da sauyin sheƙa na ɗan lokaci ba, sai dai a kan tushenta mai ƙarfi a zukatan ‘yan Najeriya, wanda a cewarsa shi ne tabbacin nasara a zaɓen shekarar 2027.
Sannan Kwamitin ya kuma yi Allah-wadai da abin da ya kira tauye dimokiraɗiyya da matsin lamba ga ‘yan adawa ta amfani da ikon gwamnati da wasu jami’an shari’a da aka zarga da rashin tsayawa kan gaskiya













































