Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran laifuka (ICPC) ta gurfanar da wasu maza biyu, Ibrahim Suleiman Umar da Tijani Adam Goni, a gaban babbar kotun babban birnin tarayya Abuja bisa zargin damfara da taikin yi da kuma yin jabun takardu na naira miliyan 4.8.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa an gurfanar da su a gaban mai shari’a B.M. Bassi kan tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi haɗin baki, karɓar kuɗi da yaudara da kuma buga jabun takardu.
A cikin bayanin ƙarar, ta ce a watan Yunin shekarar 2021, waɗannan mutane biyu sun haɗa baki wajen karɓar naira miliyan 4.8 daga wasu masu neman aiki biyu, Saifdeen Yakub da Aminu Abubakar, da sunan cewa za su samar musu aiki a Babban Bankin Najeriya (CBN) da Hukumar Haraji ta Ƙasa (FIRS), alhali sun san cewa wannan magana ba ta da tushe.
Karin labari: Kotu ta dage gurfanar da Sowore kan zargin aikata laifuka ta internet
Binciken ICPC ya ƙara gano cewa waɗanda ake tuhuma sun ƙirƙiri jabun takardun ɗaukar aiki da ake cewa daga CBN da FIRS aka fitar, tare da wata takarda da aka rubuta “Final Document List” suka nuna wa waɗanda suka yaudara da niyyar su gaskata.
Laifukan suna sabawa sashen 1(1)(a) na dokar yaudara ta 2006 tare da hukuncin da ke ƙarƙashin sashe na 1(3) na wannan doka, haka kuma sun karya sassan 363 da 364 na kundin penal code.
Da aka karanto musu ƙarar, Ibrahim Suleiman Umar da Tijani Adam Goni sun amsa laifinsu a kan tuhume-tuhume biyar.
Saboda haka ne mai shari’a Bassi ya ba da umarnin a tura su gidan gyaran hali na Kuje, ya kuma dage shari’ar zuwa ranar 29 ga Oktoba 2025 don ci gaba da sauraro.
Sai dai wani mutum na farko da ake nema a wannan shari’a, Mohammed Mustapha, ya tsere, inda hukumar ta ICPC ke ci gaba da ƙoƙarin kama shi domin fuskantar shari’a.












































