Hukumar Kwastam ta ƙasa (NCS), sashen ayyuka na tarayya (FOU) yankin B, Kaduna, ta mika wani babban samame na ƙasusuwan Jakai da fatarsa da aka kama, wanda kudinsu ya kai biliyan 3.94 ga hukumar kula da ƙa’idoji da tsare-tsaren Muhalli ta ƙasa (NESREA).
Taron mika kayan ya gudana ne a ranar Talata a Kaduna, inda mai kula da Kwastam na yankin, Mista Aminu Sule, ya gabatar da kayan da aka kwace ga wakilin NESREA a jihar, Mista Hene Emmanuel.
Kayan sun haɗa da buhunan ƙasusuwan jaki 700 da darajarsu ta kai biliyan 1.86 biliyan da kuma fatar jaki guda 2,500 da aka kiyasta darajarsu biliyan 2.07, dukkansu an kama su ne a lokuta daban-daban da jami’an sashen suka gudanar aiki.
A jawabinsa, Sule ya yi Allah wadai da haramtacciyar sana’ar kasuwancin sassan Jaki, yana mai cewa hakan barazana ce ga muhalli da tattalin arzikin al’umma.
Karanta: ICPC ta gurfanar da mutane biyu a kotu kan damfara da jabun takardar aiki na Naira miliyan 4.8
Ya bayyana cewa Jakuna na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar al’ummomin karkara a matsayin hanyar sufuri da kuma hanyar dogaro da kai.
Ya jaddada kudirin hukumar Kwastam na ganin an kiyaye doka da tsaron muhalli tare da yaƙi da laifukan da suka shafi namun daji, yana mai gargadin cewa sashen FOU yankin B ba zai lamunci Najeriya ta zama cibiyar safarar namun daji ba.
Ya kuma yaba da haɗin gwiwar hukumomi da kwazo na jami’ansa wajen cimma nasarar wannan samame, inda ya bukaci al’umma, musamman masu sufuri da masu ajiya, su rika ba da bayanai idan sun ga wanda ake zargi da safarar namun daji.
Shi ma a nasa jawabin, wakilin NESREA a jihar, Mista Hene Emmanuel, ya yaba da jajircewar Kwastam wajen dakile wannan haramtacciyar kasuwanci tare da bayyana aniyar hukumar na ganin an kiyaye doka da kuma kare jinsunan dabbobin da ke fuskantar barazanar bacewa.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa haramtacciyar kasuwancin sassan Jaki, musamman fatar Jaki da ƙasusuwansa ya ƙaru a ‘yan shekarun nan saboda ƙaruwar buƙata a wasu sassan Asiya.
NAN













































