An mayar da zaman sulhu tsakanin PENGASSAN da Kamfanin Dangote zuwa ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa

befunky 2025 8 1 16 4 27 (1)

Zaman sulhu tsakanin shugabannin ƙungiyar manyan ma’aikatan Man Fetur da iskar Gas ta ƙasa (PENGASSAN) da mahukuntan kamfanin matatar man Dangote da aka shirya a ranar Talata, an mayar da shi ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa (NSA).

Rahotanni sun nuna cewa zaman dai yana gudana ne a sirri, ba tare da manema labarai ba.

Ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi Mohammed Dingyadi, tare da wasu daga cikin shugabannin PENGASSAN da suka isa wajen taron tun da farko, sun tafi ofishin NSA domin ci gaba da tattaunawa.

Cikakken bayani kan sakamakon taron zai biyo baya.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here