Majalisar Wakilai ta nemi a tsaurara hukunci ga masu yin jabun takardun karatu

HOUSE OF REPS MEMBERS 720x430

Kwamitin haɗin gwiwa na majalisar wakilai da ke binciken zargin sayar da takardun shaidar karatu a manyan makarantu ya nemi gwamnati ta ƙara tsaurara hukunci ga duk wanda aka kama da laifin yin jabun takardun karatu.

Shugaban kwamitin, ɗan majalisar Abubakar Fulata daga jihar Jigawa, ya bayyana haka bayan ziyarar aiki da suka kai wasu manyan makarantu a jihar Legas, ciki har da jami’ar Legas, kwalejin fasaha ta Yaba, jami’ar Caleb, da jami’ar jihar Legas.

Fulata ya tunatar da cewa a da ɗalibai kan yi karatu da himma sannan su rubuta jarrabawa kafin a ba su takardar digiri, amma yanzu wasu suna neman hanya ta zamba domin samun takardu ba tare da cancanta ba.

Ya ce wannan binciken na faruwa ne sakamakon wani rahoton bincike da ɗan jarida ya fitar, wanda ya tona asirin yadda wasu ke sayen takardun karatu daga jami’o’i da kwalejoji ba bisa ka’ida ba.

Fulata ya bayyana damuwarsa cewa wasu mutane suna da takardar digiri, har ma an tura su yin bautar ƙasa, amma ba su iya rubuta sunansu yadda ya kamata balle su kare abin da suka ce sun karanta.

Ya ce hakan babban abin takaici ne ga martabar cibiyoyin ilimi na ƙasar.

Ya kara da cewa matsalar ta fi muni idan jami’an makarantu ko ma’aikata na taimakawa wajen aikata irin wannan laifi, inda ya bukaci hukumomin makarantu su ƙarfafa matakan tsaro a kan takardun shaidar digiri domin tabbatar da sahihancinsu cikin sauƙi.

Fulata ya jaddada cewa dole ne gwamnati ta ɗauki tsauraran matakai da hukunci mai tsanani ga duk wanda aka kama da jabun takarda ko taimakawa wajen aikata hakan, domin kare mutuncin tsarin ilimi a Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here