Hukumar kula da Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta bayyana cewa ta amince da kashe naira biliyan 28 domin sayen mita ga dukkan masu amfani da wutar lantarki da ke cikin rukuni A waɗanda ba su da mita, ba tare da an caje su ko sisin kobo ba.
Wannan sanarwar ta fito ne a cikin wani umarni mai taken aiwatar da tsarin “Tranche B” na shirin Asusun Siyan Mita (MAF) da hukumar NERC ta fitar, inda mataimakin shugaban hukumar, Musiliu Oseni, da kwamishinan doka, lasisi da bin ƙa’ida, Dafe Akpeneye, suka sanya hannu.
A cewar hukumar, kuɗin da aka ware a ƙarƙashin wannan sabon mataki na “Tranche B” na shirin MAF, ba wai kawai za su taimaka wajen samar da mita ga duk masu amfani da wutar da ke cikin rukuni A ba, har ma za su hanzarta rufe gibin rashin mita ga masu amfani da ke cikin rukuni B.
Hukumar ta ƙara da cewa za a raba naira biliyan 28 ɗin bisa ga irin gudunmawar da kowace kamfanin rarraba wutar lantarki (DisCo) ta bayar.
NERC ta bayyana cewa wannan umarni yana da nufin samar da tsarin aiwatarwa mai gaskiya da bayyana kowane mataki, tare da fayyace sharudda da hakkokin kamfanonin rarraba wutar lantarki da masu samar da kayan mita (MAP) wajen amfani da kuɗin da aka ware.
Hukumar ta kuma bayyana cewa dokar ta tanadi yadda za a kula da yadda ake kashe kuɗin, rahotanni, da kuma kimanta yadda ake aiwatar da shirin domin tabbatar da gaskiya, inganci da ingantaccen amfani da kuɗin asusun MAF.
A cikin rahoton, NERC ta tuna cewa a watan Afrilu na shekarar 2024, daga cikin naira biliyan 21.8 da aka tara a asusun MAF, ta saki naira biliyan 21 ga kamfanonin rarraba wutar lantarki domin siyan mita a matakin farko, wato “Tranche A”, yanzu kuma an sake sakin naira biliyan 28 a mataki na biyu “Tranche B”.
Hukumar ta bayyana cewa tsarin MAF zai bai wa harkar samar da wutar lantarki ta ƙasa (NESI) damar jawo ƙarin jarin masu zuba hannun jari domin samar da mita ta hanyar hanyoyin samun kudaden shiga da tsarin ya kirkira.
Ta kuma ce akwai buƙatar gaggawa wajen rufe gibin rashin mita ga duk masu amfani da ke cikin rukuni A domin kare samun kudin shiga da kuma inganta tsarin sarrafa bukatun wutar lantarki.
NAN













































