Zargin almundahana: EFCC ta kama shugabar hukumar NSIP, Halima Shehu

Halima Shehu 675x430
Halima Shehu 675x430

Hukumar EFCC ta kama tare da tsare shugabar hukumar ba da tallafin dogaro da kai ta kasa NSIP, Halima Shehu da aka dakatar.

An dakatar da ita ne bisa zargin rub da ciki akan kudi naira biliyan 37 da miliyan 170 da 855 da 753, na ma’aikatar jin kai da kare afkuwar bala’u karkashin jagorancin Sadiya Umar Farouk.

Karanta wannan: Hukumar ICPC ta fara gudanar da bincike kan zargin kammala digiri cikin mako 6 a Benin

A a ranar Talata ne jami’an hukumar suka je ofishin Hajiya Halima Shehu tare da gudanar da bincike, daga bisani kuma ta isa ofishin EFCC, inda suka yi mata tambayoyi har cikin dare.

Shugaba Tinubu ne ya dakatar da ita daga mukamin babbar jami’ar hukumar NSIPA watanni uku da nada ta, da kuma tabbatar da ita a cikin watan Oktoba.

Karanta wannan: Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya su mayar da al’amuransu ga Allah

A baya ta taba aiki da ma’aikatar jin kai ta tarayya daga 2017 zuwa 2022.

Rahotanni sun ce shugabar ta NSIPA da aka dakatar na shirin gudanar da taron manema labarai ne a ranar Talata, lokacin da jami’ai daga hukumar EFCC suka je ofishinta dake Abuja.

Jaridar Punch tace wata majiya na cewa an samu rashin jituwa tsakanin Halima Shehu da ministar jin kai ta yanzu, Dakta Betta Audu tun lokacin da ta kama aiki bisa zargin cewa ita kadai tana yin amfani da kudaden hukumar wadanda aka tanada don bayar da tallafi ga jama’a.

Karanta wannan: Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa ta bada Umarnin rufe Jami’o’i

An kafa shirin ne don tallafa wa miliyoyin ‘yan Najeriya domin su fita daga kangin talauci da kuma samar da sana’o’i ga talakawa da ‘yan kasa marasa galihu.

Hukumar ce kuma ke da alhakin kula da shirye-shiryen yaki da fatara da talauci kamar shirin ciyar da dalibai ‘yan makaranta da sauransu.

Rahotanni na baya-bayan nan sun nuna cewa Halima Shehu yayin wani taron manema labarai a Abuja, tana jaddada kudurinta na tabbatar da gaskiya wajen aiwatar da shirin ba da tallafin kudi dala miliyan 800 na Bankin Duniya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here