Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya tashi daga Abuja zuwa birnin Abidjan na Côte d’Ivoire a ranar Lahadi domin wakiltar shugaban ƙasa Bola Tinubu a bikin rantsar da Alassane Ouattara a wa’adinsa na huɗu a matsayin shugaban ƙasar.
Shettima zai bi sahun sauran shugabanni a fadin nahiyar Afirka da sauran su domin shaida bikin rantsuwar a ranar Litinin 8 ga watan Disamba, 2025, a fadar shugaban kasa da ke Abidjan.
Alassane Ouattara ya lashe kujerarsa ta shugabanci a ranar 25 ga Oktoba, 2025, inda Côte d’Ivoire ke da kyakkyawar alaƙar Diflomasiyya da Najeriya.
Najeriya da Côte d’Ivoire na gudanar da muhimman ayyukan haɗin gwiwa a cikin ECOWAS da Tarayyar Afirka, musamman kan tsaro, kasuwanci da cigaban tattalin arziki, waɗanda aka tsara a yarjejeniyoyi daban-daban da kuma Kwamitin Haɗin Gwiwa na ƙasashen biyu.
Haka kuma, akwai kyakkyawar alaƙar kasuwanci da zamantakewa tsakanin al’ummomin ƙasashen, musamman ma sakamakon yawan ’yan Najeriya da ke zaune a Côte d’Ivoire.
Shettima ya tafi tare da Omar Aliyu Touray, shugaban Hukumar ECOWAS, da Sanata Abubakar Sani Bello, shugaban kwamitin harkokin ƙasashen waje na majalisar dattawa, da Usman Zannah, ɗan majalisa daga mazabar Kaga/Gubio/Magumeri a majalisar wakilai.
Ana sa ran mataimakin shugaban ƙasa zai dawo Abuja bayan kammala bikin rantsar da shugaba Ouattara.













































