Yunkurin juyin mulki: Yadda Tinubu ya taimaka wajen kare Dimokuraɗiyyar ƙasar Benin – fadar shugaban ƙasa

Bola Tinubu Tinubu uk 750x430

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa bayan samun buƙatu biyu daga hukumomin ƙasar Benin, shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci jiragen yaki na rundunar sojin saman Najeriya da su shiga ƙasar domin kwace sararin samaniyarta tare da korar waɗanda suka yi yunkurin juyin mulki daga gidan talabijin na ƙasa da kuma sansanin soja da suka tattaru.

Fadar ta sanar da cewa shugaban ƙasa ya yaba da saurin martanin dakarun Najeriya wajen cika wannan umarni domin kare Dimokuraɗiyyar shekaru 35 da ƙasar Benin ke da ita.

Hukumomin ƙasar Benin sun buƙaci taimakon gaggawa ta hanyar wasiƙar Diflomasiyya, domin tabbatar da tsare tsarin mulki, kariya ga hukumomin gwamnati da kuma tsaron jama’a.

Fadar shugaban ƙasa ta ce ƙasar Benin ta kuma nemi a tura jiragen yakin Najeriya cikin sararin samaniyarta domin sa ido da gudanar da ayyukan gaggawa ƙarƙashin jagorancin hukumomin ƙasar Benin.

Haka kuma, an buƙaci tura dakarun ƙasa na Najeriya domin aiki bisa umarnin kwamandan sojin ƙasar Benin wajen kare hukumomin gwamnati da hana ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai samun nasara.

Babban hafsan tsaron Najeriya Janar Olufemi Oluyede ya ce an aiwatar da dukkan buƙatun da aka nema, tare da tabbatar da kasancewar dakarun ƙasa na Najeriya a cikin ƙasar Benin domin tallafa wa gwamnati wajen daidaita al’amura.

Karanta: Jamhuriyar Benin ta kama sojoji masu tarin yawa saboda yunƙurin juyin mulki

Ya ce aiki ne na bin umarnin shugaban ƙasa kuma rundunar ta aiwatar yadda ya kamata.

A safiyar Lahadi ne wasu sojoji ƙarƙashin jagorancin Kanal Pascal Tigri suka mamaye gidan talabijin na ƙasar Benin, inda suka sanar da kifar da gwamnatin shugaban Patrice Talon tare da dakatar da dukkan hukumomin Dimokuraɗiyya.

Bayan wasu sa’o’i ne dakarun gwamnati, tare da taimakon Najeriya, suka kwato ikon gidan talabijin suka kuma tarwatsa waɗanda suka yi yunkurin juyin mulkin.

Shugaban ƙasa Tinubu ya yaba da jajircewar dakarun Najeriya da suka taimaka wajen dawo da tsarin mulki a ƙasar makwabciya, tare da bayyana cewa aikin da aka yi ya kasance bisa ka’idojin yarjejeniyar ECOWAS kan Dimokuraɗiyya da kyakkyawan shugabanci.

Ya kuma ce Najeriya na tare da gwamnatin da al’ummar ƙasar Benin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here