Jamhuriyar Benin ta kama sojoji masu tarin yawa saboda yunƙurin juyin mulki

Coup in Benin Republic 1 750x430

Gwamnatin Sojin Jamhuriyar Benin sun kama tarin sojoji masu yawa da suka haɗa da jagororin da suka shirya yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba.

Adadin da aka tsare ya kai mutum goma sha uku, inda ɗaya daga cikinsu tsohon soja ne, sauran kuwa duka sojoji ne da ke cikin aiki.

Kamen na su ya faru ne bayan wasu jami’an soji sun bayyana a talabijin na ƙasar da safiyar Lahadi, inda suka sanar da kifar da gwamnatin shugaba Patrice Talon tare da rushe dukkanin muƙaman gwamnati.

Labari mai alaƙa: Da zafi-zafi: Sojoji sun karɓe mulki a Jamhuriyar Benin

Jami’an sun bayyana kansu a matsayin “Kwamitin Soji na Sake Farfaɗo da kasar”, suna iƙirarin cewa sun karɓi mulki.

Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa shugaba Talon yana cikin koshin lafiya, kuma rundunar sojin da ta kasance a kan biyayya tana mayar da doka da oda a faɗin ƙasar.

Fadar ta bayyana wannan lamari a matsayin aikin kananan ƙungiya da ba su da tasiri sosai wajen kawo barazana ga tsarin gwamnati.

Gwamnatin ta ce rundunar sojin ƙasa na ci gaba da kwato iko, kuma birni da ƙasar baki ɗaya suna cikin tsaro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here