Ribaɗu ya tattauna matsalolin tsaro da tawagar majalisar dokokin Amurka a Abuja

NSA Nuhu Ribadu noted that the visit follows prior meetings in Washington D.C

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya karɓi tawagar majalisar dokokin Amurka a Abuja domin ci gaba da tattaunawa kan haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.

Ziyarar ta biyo bayan ganawarsu ta baya da suka yi a Washington, DC kan batutuwan tsaron da suka shafi ƙasashen biyu.

Tawagar ta haɗa da Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani da Riley M. Moore, tare da halartar jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills.

Ganawar ta mayar da hankali kan yaki da ta’addanci, tabbatar da zaman lafiya a yankin, da kuma ƙarfafa alaƙar tsaron ƙasashen biyu.

Ribadu ya bayyana cewa tattaunawar za ta ƙara gina amincewa da haɗin kai wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Ganawar ta gudana ne a lokacin da ake fuskantar ɗan tashin hankali a harkokin diflomasiyya sakamakon matakin shugaban Amurka Donald Trump na maido da Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kallon suna da matsalolin ’yancin addini tare da barazanar yiwuwar tsoma bakin soji.

Karanta: Ribadu zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa aikin haɗin gwiwa da ƙasar Amurka – Fadar shugaban ƙasa

Gwamnatin tarayya ta nace cewa matsalolin tsaro ba su takaita ga addini guda ba, domin rikice-rikicen sun shafi jama’a daga bangarori daban-daban a faɗin ƙasa.

Duk da matsin lambar ƙasashen duniya, gwamnati na ci gaba da neman haɗin gwiwar tsaro da diflomasiyya daga abokan hulɗa na ƙasashen waje.

A ranar 20 ga Nuwamba, Ribadu ya gana da sakataren yaƙi na Amurka, Pete Hegseth, a Pentagon domin tattauna dabarun haɗin kai wajen magance ƙalubalen tsaro a Najeriya.

A ranar 27 ga Nuwamba kuwa, shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da kafa ɓangaren Najeriya na kwamitin haɗin gwiwar tsaro na Najeriya da Amurka, wanda aka cimma a ziyarar tawagar Najeriya ta baya a Washington ƙarƙashin jagorancin Ribadu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here