Ƙungiyar dattawan Arewa, ta buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, da ya yi burabus daga muƙaminsa sakamakon ƙaruwar kashe-kashen mutane da ake samu ba gaira babu dalili, musamman a yankin Arewacin Najeriya.
Kiran na zuwa ne ta cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a yau Talata mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun ƙungiyar Dakta Hakeem Baba Ahmed.
“Salon jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, ba ya nuna cewa za a iya kawo ƙarshen matsalar tsaro da ake fama da ita wadda a kullum ta ke ƙara ta’azzara a kasar nan” a cewar Hakeem Baba.
Ba zamu iya ci gaba da zuba ido ana kashe mu da iyalanmu, ana garkuwa damu da iyalanmu ba, duk abubuwa sun sukurkurce, ya kamata a barmu mu rayu da iyalanmu cikin salama.
“Kundin tsarin mulkin kasar mu ya ware wani sashi da ya bai wa shugabanni damar sauka daga kan muƙaminsu matukar suka gaza gudar da mulkin su yadda ya dace”. Inji Baba Ahmed.
Sanarwar ta ƙara da cewa a dai-dai wannan lokacin shugaba Muhammadu Buhari ba shi da wani zaɓi face ya sauka daga kan kujerarsa ta Shugabancin ƙasa sakamakon gaza samarwa al’ummarsa tsaro da zaman lafiya mai ɗorewa.
“Kungiyar mu tana sane da halin da al’ummar kasa ke ciki, kuma ba za su iya ci gaba da jure gashin kumar da ake yi musu har zuwa shekarar 2023 lokacin da wa’adin mulkinsa zai ƙare ba”.