Sanata Barau ya yaba wa Buhari kan amincewa da gina kwalejin fasaha ta tarayya a Kano

Senator Barau Jubrin
Senator Barau Jubrin

Shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da kasafin kuɗi, Sanata Barau Jibrin, ya yaba wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bisa amincewa da kafa kwalejin fasaha ta gwamnatin tarayya a Kano.

Sanatan mai wakiltar Kano ta Arewa a majalisar dattawa a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata ya ce, kafa makarantar ba ƙaramin abu ba ne da zai inganta harkar ilimi a jihar da kuma samar da karin ayyukan yi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Kano a matsayin cibiya mai nagarta, kafa kwalejin a jihar zai bunƙasa masana’antu da samar da kwararrun ma’aikata tare da haɓɓaka fasahar ƙere-ƙere don tallafa wa ɓangarorin masana’antu da hidima ga jihar.”

” Idan an kafa kwalejin za ta samar da kwasa-kwasai da darussan fannin fasaha da sarrafa ilimin kimiyya da sauran fannonin karatu”.

A cewar sanarwar, tun a shekarar 2017 ne aka fara ƙoƙarin kafa kwalejin fasahar ta gwamnatin tarayya wanda a lokacin Sanatan ya kai ƙudirin kafa ta a zauren majalisar wakilai ta 8.

Sanarwar ta kara da cewa, wannan mafarki ne da fatan al’ummar Kano na ganin an samu ƙarin kwalejin ta tarayya.

Solacebase ta tuno da cewa majalisar dattijai a watan Nuwamba shekarar 2018 ta zartar da ƙudirin kafa makarantun fasahar guda biyar, inda za a gina ta Kano a ƙaramar hukumar Kabo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here