Yanzu-yanzu: Tinubu ya rattaba hannu kan gyaran Dokar Zaɓe wadda ta zama doka

tinubu 2 (1)

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin gyaran Dokar Zaɓe ta 2022 (wadda aka soke aka sake Ƙaddamarwa) ta 2026, wanda hakan ya mayar da shi doka.

Hakan na zuwa ne bayan Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da kudirin a ranar Talata, bayan shafe watanni ana tattaunawa a kansa.

Kudirin ya janyo muhawara mai zafi a makon da ya gabata, musamman kan yadda za a riƙa aika sakamakon zaɓe gabanin babban zaɓen 2027, inda ’yan majalisa da wasu fitattun ’yan ƙasa suka nuna sabanin ra’ayi.

A Majalisar Dattawa, zaman ya ɗauki salo mai cike da hayaniya yayin duba kudirin sashe bayan sashe, musamman a Sashe na 60, inda Sanata Enyinnaya Abaribe ya nemi a yi raba gardama kan tanadin da ya shafi aika sakamakon zaɓe ta na’urar lantarki da kuma yiwuwar komawa tsarin hannu idan aka samu matsalar cibiyar sadarwa.

Bayan ƙirga ƙuri’u, sanatoci 55 sun goyi bayan barin tanadin da ke ba da damar aika sakamako ta hannu idan tsarin lantarki ya gaza, yayin da sanatoci 15 suka nuna adawa.

Majalisar Wakilai ma ta fuskanci irin wannan takaddama, bayan da aka gabatar da ƙudirin soke matsayar da ta ɗauka a baya kan wajabta aika sakamakon zaɓe ta lantarki kai tsaye.

Lokacin da aka kada ƙuri’ar murya, masu adawa sun fi ƙarfi a ji, amma kakakin majalisar ya yanke hukuncin cewa masu goyon baya sun yi nasara, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a zauren kafin a koma zaman sirri.

Daga rattaba hannun shugaban ƙasa, dokar gyaran zaɓen ta fara aiki, wanda ake sa ran za ta yi tasiri ga shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here